Abun kunya ne yadda babu wata matatan man fetur da ke cikakken aiki a Najeriya, inji Shugaba Buhari

Abun kunya ne yadda babu wata matatan man fetur da ke cikakken aiki a Najeriya, inji Shugaba Buhari

- Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana damuwar sa game da yadda babu wata matatan man fetur na Kasar nan da take rabin aikin da ya kamace ta

- Ya yi jimami ganin yadda a lokacin mulkin sa na soja, dukkan matatun su na aiki yadda ya kamata

- Ya kuma yabawa kamfanin mai na Eni bisa yadda za ta gyara matatan Fatakwal da kuma kara gina wani

A ranar Juma'a ne Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana damuwar sa ga yadda babu wata matatan man fetur da ta ke gudanar da rabin aikin da ya kamace ta. Ya yi jimamin yadda a lokacin da ya ke mulkin soja, dukkan matatan su na cikakken aiki.

Abun kunya ne yadda babu wata matatan man fetur da ke cikakken aiki a Najeriya, inji Shugaba Buhari
Abun kunya ne yadda babu wata matatan man fetur da ke cikakken aiki a Najeriya, inji Shugaba Buhari

Mai magana da yawun Shugaban Kasa, Femi Adesina, ya bayyana cewar Buhari ya yi wannan jawabi ne yayin tarban wakilan hako man fetur daga Eni, karkashin jagorancin shugaban su, Antonia Vella.

KU KARANTA: Kotu ta yi watsi da karar da Nnamdi Kanu ya shigar kan Hukumar Soji

Buhari ya bayyana yadda a wancan zamanin, baya ga tace man fetur yadda ya kamata, a na fitar da gangan mai guda 100,000 a kullum zuwa kasuwannin man fetur na duniya.

Ya kuma yabawa Eni bisa yadda su ka dauki nauyin gyara matatan da ke Fatakwal, da kuma gina wani sabo wanda a kullum za a tace gangan mai 150,000.

Vella kuma ya bayyana cewan tuni a ka tura matasa ma su digiri guda 50 zuwa Itali domin horas da su. Za su dauki horon har na tsawon watanni 7. Ya kuma ce za a kashe dala biliyan 13 ne a gudanar da ayyukan.

Cikin ayyukan har da habaka wutan lantarki na wurin aikin su da ke yankin Delta. Za a habaka shi ne daga 500MW zuwa 1000MW, a inda za a kashe naira miliyan 750.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel