Gwamna Abubakar zai naɗa kwamishinoni 20 a sabuwar majalisarsa

Gwamna Abubakar zai naɗa kwamishinoni 20 a sabuwar majalisarsa

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, dukkanin ƙananan hukumomi ashirin na jihar Bauchi za su samu wakilai a sabuwar majalisar gwamnan jihar, Mohammed Abubakar, domin faɗaɗa wakilci da kuma samar da tushen ra'ayoyi daban-daban.

A wata sanarwar da sanadin kakakin fadar gwamnatin jihar, Abubakar Al-Sadique ya bayyana cewa, tuni gwamnan ya shirya matakai da tsare-tsaren kafa wannan sabuwar majalisar, inda zai naɗa sabbin kwamishinoni 20 domin ribatar gogayyar ƙwarewa daban-daban.

Gwamna Muhammad Abubakar
Gwamna Muhammad Abubakar

Legit.ng ta fahimci cewa, tun a yayin hawa kujerar mulkin jihar a shekarar 2015, gwamna Abubakar ya rage adadin ma'aikatu da kwamishinonin su daga 26 zuwa 16, wanda a yanzu ya buƙaci bunƙasa su.

KARANTA KUMA: Rikicin makiyaya a jihar Binuwai: Gwamna Ortom ya caccaki ministan tsaro na Najeriya

Kakakin yake cewa, gwamnan zai yi wannan garambawul ne a majalisar sa domin samun wakilai daga kowace ƙaramar hukuma ta jihar da hakan kawar da makamanciyar tuhuma da aka yiwa gwamnatin baya na nuna wariya da kuma son kai.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel