Katsina: Jami'ar tarayya ta Dutsinma ta dawo da ma'aikata 250 da aka dakatar

Katsina: Jami'ar tarayya ta Dutsinma ta dawo da ma'aikata 250 da aka dakatar

Jami'ar tarayya da ke Dutsinma a jihar Katsina ta bayyana cewa ta dawo da wasu ma’aikata 250 da shugabancin da ta gabata ta kora daga aiki ba bisa ka'ida ba. Shugaban Jami'ar ya ce tuni an biya ma’aikatan kudin alawus na su.

Jami'ar tarayya da ke Dutsinma a jihar Katsina, ta dawo da m'aikatanta 250 wadanda shugabancin jami’ar da ta shude ta sallama.

Shugaban Jami'ar, Farfesa Armaya'u Bichi ya bayyana hakan a wani taron manema labaraai a ranar Juma'a, 26 ga watan Janairu a Dutsinma.

Zaku iya tuna cewa hukumar jami’ar ta kori ma'aikatan wucin gadi wadanda ba a tabbatar da daukar su aiki ba. Shugaban ya bayyana cewa, an biya ma'aikatan da wannan lamarin ta shafa kudaden alawus na su don bunkasa halayensu da kuma tabbatar da ingantaccen aiki.

Katsina: Jami'ar tarayya ta Dutsinma ta dawo da ma'aikata 250 da aka dakatar
Jami'ar tarayya ta Dutsinma a jihar Katsina

"Shugabancin da ta shude ta kori ma'aikatan ba bisa ka'ida ba, mun fahimci cewa wannan matakin ba daidai ba ne", in ji shi.

KU KARANTA: 'Yan Najeriya mazauna Saudiyya sun yi Allah wadai da kalaman Sheik Ahmad Gumi

Bichi ya kara da cewa jama’ar har zuwa yanzu ta dauka ma'aikatan ilimi 250 da kuma fiye da 200 wadanda ba ma'aikatan ilimi ba don inganta ayyukan ilimi a jami'ar.

Bichi ya bayyana cewa jami'ar tana ba da kyautar magunguna ga marasa lafiya a yankunan kuma ta rarraba kyautar kwamfuta ga makarantun sakandare don karfafa dangantaka da ke tsakanin su da al’ummar yankin.

Legit.ng ta fahimci cewa a shekara ta 2011 aka kafa jami’ar kuma za ta yaye dalibai 500 karo na farko a ranar Asabar mai zuwa.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel