Rikicin makiyaya da manoma :Yan bindiga sun halaka Yansanda 7, Sojoji 2 a jihar Adamawa

Rikicin makiyaya da manoma :Yan bindiga sun halaka Yansanda 7, Sojoji 2 a jihar Adamawa

Akalla jami’an tsaro guda tara ne suka yi asarar rayukansu a sakamakon rikicin makiyaya da manoma daya barke a garin Numan na jihar Adamawa, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Kwamanan rundunan Sojoji dake garin Yola na jihar Adamawa, Birgediya Bello Mohammed ne ya sanar da haka a yayin wata ganawa da yayi da jama’a a garin Yola, inda yace daga cikin wadanda suka mutu akwai jami’an Yansanda guda bakwai, da jami’an Soji guda biyu.

KU KARANTA: Jihohi guda 16 sun amince a tsugunar da Makiyaya da dabbobinsu a cikinsu, ga jerin su nan

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Kwamanda Muhammed yana fadin sun shirya wannan taron ganawa da jama’a ne da nufin gargadin duk masu hannu cikin rikicin cewa daga yanzu ba sassautawa ga duk wadanda suka kama.

Rikicin makiyaya da manoma :Yan bindiga sun halaka Yansanda 7, Sojoji 2 a jihar Adamawa
Yansanda

“Rikicin da ya faro a garin Numan ya watsu zuwa kananan hukumomi guda hudu, Girei, Demsa, Lamurde da wasu sassan jihar Taraba, sai dai matakin da jami’an tsaro suka dauka da fari bai yi nasarar shawo kan matsalar ba, amma daga yanzu zamu fara gudanar da sabon tsarin yaki da duk masu hannu cikin rikicin.” Inji shi.

Birgediya Bello yace sun gano akwai hannun sarakunan gargajiya da yan siyasa cikin masu rura rikicin makiyaya da manoma, sa’annan yace sau dayawa mutane na watsa jita jita dake haifar da rashin jituwa tsakanin makiyaya da manoma.

Daga yanzu a cewar Birgediya ba zasu lamunci mutanen dake taro ba’a a kan ka’ida ba, tare hanyoyi ba tare da ka’ida ba da kuma shiga aikin jami’an tsaro yayin da suka yi yunkurin cafke masu laifi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng