Gwamnatin Najeriya ta ki amincewa da sharuddan Amurka kafin a sayar mata da jirage
- Kasar Amurka ta gindaya sharuddanta kafin taimakon Najeriya yaki da Boko Haram
- Jiragen na da matukar muhimmanci ga yaki da Boko Haram
- Kudin jiyagen ya kusa rabiin biliyan na daloli
Ministan tsaro na Najeriya, Mannir dan Ali, ya ce kasar Najeriya baza ta yarda da tsauraran matakan da aka gindaya mata ba, kafin a sayar mata da jiragen saman yaki da ta'addanci.
Jiragen na kirar A-29, Super Tucano, guda 12 da Najeriyar take so daga Amurka, sun kai dala miliyan $499m, kusan Naira biliyan 160 kenan.
Daga cikin bukatun Amurka shine, Amurkar, baza ta koya wa sojin Najeriya aiki da jirgin ba, ba kuma ata aiko jiragen ba sai bayan 2020, wadda ministan yace baza-ta sabu ba sam.
DUBA WANNAN: Boko Haram na kara karfi - Bincike
Sun kuma ce baza su bar sojin Najeriya bin kadin inda ake hada jiragen ba, domin tabbatar da ingancinsu, ministan ya fada, ya kuma ce ai in kasar Rasha ne, sun bar masu kula daga Najeriya sun zauna din-dindin har aka gama kera wa Najeriya nata jiragen masu saukar angulu.
Ministan ya dai ce, zai gana da jakadan Amurkar domin bin bahasi, da ma rage wasu daga cikin matakan.
Ita dai Amurka, ta dakatar da wannan sayarwa ne, tun lokacin da sojin Najeriya suka kashe mutum 150 bisa kuskure, a Rann, a sansanin 'yan gudun hijira, da ma kuma rahotannin Najeriyar na tauye hakkin bil'adam a yakin ta da ta'addanci.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng