Sanata Lado ya sauya sheƙa a yayin da Kwankwaso zai ziyarci jihar Kano

Sanata Lado ya sauya sheƙa a yayin da Kwankwaso zai ziyarci jihar Kano

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, jiga-jigan jam'iyyar APC ta jihar Kano za su gudanar da tarukan siyasa har kashi biyu daban-daban, inda gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje da kuma sanata mai wakiltar jihar ta Tsakiya, Rabi'u Musa Kwankwaso zasu jagoranta.

Taron gwamnan jihar wato na Gandujiyya, zai karbi tsohon sanata mai wakilta jihar ta Tsakiya, Sanata Basheer Garba Lado, wanda ya tattaro sama da mambobi 100, 000 da suka yi sauyin sheƙa daga jam'iyyar adawa ta PDP zuwa APC.

A ranar 28 ga watan Janairu ne, za a gudanar da taron Gandujiyya a garin Bichi, inda za a baiwa 'yan takara tutocin jam'iyyar na zaben ƙananan hukumomi da za a gudanar a ranar 29 ga watan Janairun, wanda daga bisani kuma su shilla zuwa garuruwan Gwarzo da kuma Kwanar Dangora domin gudanar da wani taron.

Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso
Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso

Jaridar ta kuma ruwaito cewa, za a gudanar da makamancin wannan taro a garin Wudil a ranar 31 ga watan Janairun, inda makamancin wannan taruka zasu ci gaba da gudana har zuwa ranar 8 ga watan Fabrairu.

Legit.ng ta fahimci cewa, za a gudanar da taron Kwankwasiyya domin girmamawa ga tsohon gwamnan jihar Rabi'u Kwankwaso a ranar 30 ga watan Janairu.

KARANTA KUMA: Gwamnatin tarayya za ta baiwa 'yan Najeriya 8m kulawar lafiya kyauta a 2018

Majiyar rahoton ta kuma bayyana cewa, baya ga sauyin sheƙa na Sanata Lado, akwai kuma tsohon dan majalisar wakilai da shugabannin ƙananan hukumomi na jam'iyyar da adawa da za suyi waiwaye adon tafiya zuwa jam'iyyar ta APC.

Jaridar ta daily ta hasashen cewa, a sakamakon hamayya dake tsakanin wannan jiga-jigai na jam'iyyar APc, ta yiwu a samu labari akasin na farin ciki a yayin gudanar da wannan taruka, wanda a baya arangama tsakanin magoya bayan su suka baiwa hammata iska tare da zubar jinin juna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: