Wata tsohuwa tukuf a Kasar Kenya ta koma Makarantar Firamare

Wata tsohuwa tukuf a Kasar Kenya ta koma Makarantar Firamare

- Tsohuwa ‘Yar shekara 90 ta shiga Makarantar Firamare a Kenya

- Wannan Dattijuwar tana da sha’awar koyon karatu da ma rubutu

- Yanzu haka ajin ta daya da wasu daga cikin jikokin ta a Duniya

Mun samu labari cewa wata Baiwar Allah ‘Yar shekara 90 ta shiga Makarantar Firamare domin yin ilmin Boko a kasar Kenya. Watakila dai duk Duniya babu ‘Daliba mai irin yawan shekarun ta.

Wata tsohuwa tukuf a Kasar Kenya ta koma Makarantar Firamare
Dattijuwa cikin aji tare da jikokin ta wajen neman ilmi

Priscilla Sitenei wanda tana da yara da jikoki rututu ta shiga makarantar Boko ne a kasar Kenya duk da ta kusa kai shekaru 100 a Duniya. Baiwar Allah ta koma karatu ne domin ta iya karanta littafin injila mai tsarki na Kiristoci kafin ta bar Duniya.

KU KARANTA: Mai ba Gwamnan Legas shawara ya yanke jiki ya mutu

Bayan nan kuma Dattjiuwar ta na da sha’awar iya amfani da wayar salulata zamani ta aikawa Jama’a sako cikin sauki. Don haka ne ta shiga makaranta domin a fara koya mata karatu da rutubu daga farko kamar yadda mu ka ji daga Tuko.co.ke.

Priscilla ta fito ne daga Yankin Eldoret na Uasin Gishu da ke cikin Kasar Kenya. Jama’a da dama dai su na kiran ta ‘gogo’ saboda ta tsufa. Yanzu haka dai ajin ta daya da wasu jikojin ta 7. Gogo ta yi shekaru sama da 65 tana aikin ungonzoma.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng