Yara miliyan 25 ne za'a yi wa rigakafin cutar shawara watau yalo fiba

Yara miliyan 25 ne za'a yi wa rigakafin cutar shawara watau yalo fiba

- Cutar Yalo Fiba na kai hari ga kananan yara a duk shekara

- Za'a yi wa yara miliyan 25 riga-kai a birni da kauye

- Manya da yara na kamuwa da cutar amma ta fi lahanta yara

Yara miliyan 25 ne za'a yi wa rigakafin cutar shawara watau yalo fiba
Yara miliyan 25 ne za'a yi wa rigakafin cutar shawara watau yalo fiba

Cutar Yellow fever, watau shawara, wadda kan sa ido yayi yellow shar, sauro ke kawo ta, duk da cewa a da an zaci wata cuta ce ta aljannu ko sammu. Ita ma zazzabi ne kamar sauran cutuka da sauro ke yada wa.

Yanzu dai a Najeriya za'a yi maganin cutar ta hanyar yi wa mutum miliyan 25 riga-kafi, a birni da kauyuka. Ana kuma ffata, jama'a sun waye zasu bari a yi musu da iyalansu, ba kamar da ba da ake tsoron baturen riga-kafi.

Cikin kwanakin da ke tafe, ana sa ran yi wa mutum miliyan 8.6 riga-kafin na shawara, yayin da a tsawon shekarar kuma ake son yi wa mutum fiye da miliyan 25 musamman a jihohin da suka fi fuskantar kasadar barkewar annobar cutar. Bayanai na cewa za a yi rigakafin ne ga 'yan shekara daya zuwa 'yan shekara 30.

DUBA WANNAN: Za'a yi wa APC taron dangi kamar yadda aka yi wa PDP a baya

Hukumomin Nigeria tare da hadin gwiwar hukumomi na kasa da kasa, ciki har da Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, Da Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, na kaddamar da aikin rigakafin cutar shawara, wanda shi ne aikin riga-kafin cutar mafi girma a fadin kasar a tarihinta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel