Makiyaya sun kai wani sabon hari jihar Binuwai
Mutane biyu ne suka rasa rayukan su da suka haɗar da wani jami'in ɗan sanda a wani sabon hari da makiyaya suka zartar a ƙaramar hukumar Guma ta jihar Binuwai.
Ƙananan hukumomin Guma da Logo sune yankunan dake fama da azabcin hare-haren makiyaya tun gabatar sabuwar shekarar nan, inda wannan sabon hari ya afku a tsakanin daren ranar larabar da ta gabata da kuma safiyar yau alhamis.
Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, ba a cimma nasara ba a yayin yunƙuri na tuntuɓar kakakin 'yan sandan jihar, ASP Moses Yamu, a wayarsa ta salula domin samun kanin rahoton.
Sai dai gwamnan jihar Samuel Ortom, ya tabbatar da afkuwar wannan hari a yayin da yake tarbar tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso wanda ya kai ziyarar jaje da kuma ta'aziyar rayukan da suka salwanta a rikicin makon da ya gabata.
Gwamna Ortom yake cewa, "a halin yanzu da nake ganawa da ku, rayuka biyu sun salwanta da ya haɗar har da jami'in ɗan sanda ɗaya a karamar hukuma ta ta Guma."
KARANTA KUMA: Za mu ƙauracewa cin naman shanu - Al'ummar kudancin Najeriya
A nasa jawabin, tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Kwankwaso, yayi tir da wannan hare-haren ta'addanci a jihar Binuwai da kuma sauran sassan ƙasa baki ɗaya.
Sanata Kwankwaso ya kuma bayar da tallafin buhunan shinkafa 1200 ga 'yan gudun hijira dake jihar wanda adadin su ya tasar ma mutane dubu tamanin.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng