Gwamna Masari zai yi wasu sabbin nadi a Katsina

Gwamna Masari zai yi wasu sabbin nadi a Katsina

Gwamna Masari ya amince zai cika gurubin wasu sakatarori na dindindin da kuma nada wasu sabo su hudu a jihar. Har zuwa yanzu sanarwa daga gwamnati ba ta bayyana ranar da za a rantsar da sabbin sakatarorin ba.

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya amince da nada sabbin sakatarori na dindindin su hudu a ma’aikatar ta Jihar bayan da aka dakatar da wasu tsoffin sakataren.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito cewa wannan ya ƙunshi ne a cikin wata sanarwa da aka bayar a ranar 23 ga watan Janairu, 2018 wanda sakataren harkokin gudanarwa a ofishin shugaban ma’aikata, Alhaji A. D. Umar ya sanya hannu.

A cewar sanarwar, wadanda aka nada su ne Muntari Danladi, wanda har zuwa yanzu ya kasance darektan gudanarwa da samar da kayayyaki a ma'aikatar kudi da Buhari Salisu Yamel, wanda har zuwa lokacin da aka nada shi kasance darekta a ma’aikatar ilimi karkashin ‘Zonal Education Quality assurance’, Mani.

Gwamna Masari zai yi wasu sabbin nadi a Katsina
Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari

Sauran sun hada da Sani Isyaku Masari wanda aka sake nada shi da kuma Sulaiman yakubu Safana wanda shi ma an sake nada shi.

KU KARANTA: Obasanjo zai kafa kungiya don tsige Buhari daga mulki

Sanarwar ta bayyana cewa za a sanar da ranar da za a rantsar da su a daidai lokaci.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng