Wani Saurayi ya dirka ma budurwarsa ciki, kuma ya kashe mahaifinta

Wani Saurayi ya dirka ma budurwarsa ciki, kuma ya kashe mahaifinta

Rundunar Yansandan jihar Katsina ta cika hannu da wani matashi mai shekaru 22 da ake zargi da hallaka mahaifin budurwarsa a unguwar Dutsen Reme dake garin Bakori, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito matashin mai suna Maruf Yakubu da ya fito daga jihar Zamfara yana soyayya ne da wata budurwa Aisha Yakubu, sai dai mahaifinta Yahaya Yakubu ya nuna rashin amincewarsa da wannan saurayi na ta.

KU KARANTA: Dalibi mai shekaru 15 ya bindige yan ajinsu mutum 2, ya raunata mutane 17

Ana cikn haka sai wata rana Malam Yahaya ya tunkari Maruf, kuma ya fada masa baya kaunarsa da yarsa Aisha, don haka ya rabu da ita, kada ya sake zuwa wajenta, amma sai Saurayin ya bayyana ma sha ba zai ya rabuwa da it aba, kuma duk abinda za’a yi sai ya aure ta.

A yayin wannan cacar baki ne sai matashin ya shaida ma mahaifin budurwar tasa cewa, ya riga yayi ma ta ciki, don haka tunda tana dauke da cikinsa, sai ya aure ta. Jin haka ya sanya malam Yahaya cikin rudani da tsabar bakin ciki, nan take zuciyarsa ta buga ya yanke jiki ya fadi.

Bayan an garzaya da shi Asibiti ne ya mutu a can, kamar yadda Kaakakin rundunar Yansandan jihar, DSP Gambo Isah ya tabbatar, kuma yace Yasanda sun kama Saurayin, budurwar da kuma wani makwabcinsu Yahaya Mani.

Kaakakin yace da zarar sun kammala bincike za’a gurfanar da wadanda ake zargi da hannu cikin kisan Malam Yahaya Yakubu gaban kuliya manta sabo don tabbatar da an yi adalci.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: