Dan majalisa Ado Doguwa ya gargadi Obasanjo game da zantukan da yake furtawa

Dan majalisa Ado Doguwa ya gargadi Obasanjo game da zantukan da yake furtawa

Bulaliyar majalisar wakilan Najeriya, Ado Alhassan Doguwa ya bayyana batutuwan da wasikar da Obasanjo ya aika ma shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin zance mara amfani.

Doguwa ya bayyana haka ne yayin ganawa da manema labaru a garin Abuja, inda yace wannan wasikar ta kara nuna ma yan Najeriya mugun halayyar tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, kuma yayi kira ga yan Najeriya su yi watsi da shi.

KU KARANTA: Cutar zazzabin bera: Gwamnati ta sanya dokar hana shan Garin-Kwaki

Daily Trust ta ruwaito Doguwa na fadin abinda Obasanjo ya yi, yayi daidai da batun da ake yin a cewa akwai masu nuna adawa da nasarorin da shugaban kasa yake samu a yakin da yake yi da cin hanci da rashawa.

Dan majalisa Ado Doguwa ya gargadi Obasanjo game da zantukan da yake furtawa
Doguwa

“Obasanjo yayi kaurin suna wajen furta kalaman siyasa marasa kan gado, don haka ya sani ba isa ya zame ma shugaban kasa Muhammadu Buhari tarnaki ba game da zarcewa bisa mulki da yan Najeriya ke bukatar yayi, don gyaran irin barnar da Obasanjo yayi, da ire irensa.” Inji Doguwa.

Doguwa ya cigaba da shaida ma majiyar Legit.ng cewa Obasanjo ba shi da hurumin furta irin kalaman da yake yi a kan siyasar Najeriya, musamman idan aka duba ire iren badakalar da aka tafka a zamanin mulkinsa, daga 1999-2007.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng