Obasanjo ya so ya maida Shugaba Buhari yaron sa ne – Fulani Makiyaya

Obasanjo ya so ya maida Shugaba Buhari yaron sa ne – Fulani Makiyaya

- Makiyaya Fulani sun nemi Shugaba Buhari yayi watsi da wasikar Obasanjo

- ‘Yan Miyetti Allah sun ce Cif Obasanjo na neman wanda zai rika juyawa ne

- Daily Trust ce ta zanta da Shugaban ‘Yan Kungiyar Miyetti Allah kwanan nan

Kungiyar ‘Yan Miyetti Allah ta Makiyayan Najeriya a reshen Jihar Nasarawa sun bayyana dalilin da ya sa tsohon Shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya juyawa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari baya.

Obasanjo ya so ya maida Shugaba Buhari yaron sa ne – Fulani Makiyaya
Ashe Obasanjo yayi kokarin maida Buhari dan-waken zagaye

MACBAN ta bakin Shugaban ta na Jihar Nasarawa Muhammed Hussaini tace Obasanjo yana neman Shugaban da zai rika kadawa yadda ya ga dama ne shiyasa ya aika wasika inda yake nuna gazawar kuma ya shawarce sa da ya hakura da takarar 2019.

KU KARANTA: Ba wasikar Obasanjo ta kai su Tinubu wajen Buhari ba

Muhammed Hussaini ya nemi Shugaban kasa Buhari ya rabu da Obasanjo ya sake tsaya takara a zabe mai zuwa. Makiyayan sun ce Obasanjo ya so ya rika yi da Shugaba Buhari ne kamar dan-waken zagaye watau sai yadda yace yayi sannan zai yi.

A cewar Shugaban na Miyetti Allah, tsohon Shugaban kasa yayi wannan lokacin da ya daura Marigayi Umaru Yar’adua kan mulki. Bayan ya rasu abin bai yiwu ba, sai ya koma kan Shugaba Jonathan wanda shi ma ya gaza juya sa kamar yadda yake so.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng