Ministan sadarwa ya ji kunya a taron mako-makon Gwamnatin Tarayya kan takakar Shugaba Buhari
- An hana a raba hulunan tazarce Shugaban kasa Buhari a taro
- Ministan sadarwa Shitu ya kawo hulunan kamfen zaben 2019
- Ba a bari an rabawa Ministoci hulunan a cikin fadar Villa ba
Jaridar Daily Trust ta kasar nan ta bayyana yadda Ministan Shugaban kasa Buhari ya kunyata a wajen taron FEC na Majalisar zartarwa da ake yi a kowace Laraba.
Ministan sadarwa na Najeriya Adebayor Shitu ya ji kunya ne a taron mako-makon Gwamnatin Tarayya inda aka hana sa shiga da hulunan da ya kawo na yakin neman zaben Shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma Mataimakin sa Farfesa Yemi Osinbajo.
KU KARANTA: Wasu Ministoci na goyon bayan Shugaba Buhari ya sake takara
Kamar yadda Majiyar mu ta bayyana, Sakataren Gwamnatin Tarayya watau Boss Mustafa ne ya hana a raba wadannan huluna da aka kawo wajen taron Ministocin. Shitu ne dai jagoran yakin neman zaben Shugaba Buhari a Yankin Yarbawa a 2019.
Shitu wanda yake neman Gwamnan Jihar Oyo bai yi nasarar rabawa Ministocin hular tazarcen ba amma dai ya shigo taron da na sa. A baya dai Sakataren Gwamnatin Tarayya Mista Boss ya bayyana cewa Shugaba Buhari ya ci zaben 2019 ya gama kawai.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng