Mutane 9 aka kashe tare da sace wasu 7 a sabon harin da aka kai jihar Adamawa
- Wasu 'yan bindiga da ya zuwa yanzu ba'a san ko su waye ba sun kai hari a jihar Adamawa
- Sun kai harin ne a daren jiya, Talata, kuma sun kashe mutane tara tare da sace yara bakwai
- Hukumar 'yan sanda ta tabbatar da faruwar al'amarin tare bayyana cewar tana bincike a kan lamarin
Wasu 'yan bindiga da ya zuwa yanzu ba'a san ko su waye ba sun kai hari wani kauye mai suna Iware dake kan hanyar Furfore zuwa Jada a jihar Adamawa tare da kashe mutane tara da sace yara bakwai.
Wani dan kungiyar sintiri a kauyen ya sanar da majiyar mu cewar 'yan bindigar sun kai harin ne a daren jiya, Talata, kuma sun tsere da wasu yara bakwai bayan kisan wasu mutanen tara.
Majiyar mu ta ce kauyen da aka kaiwa harin na wasu Fulbe ne da basu dade da kafa shi ba, kusa da Beti Verre, a tsakanin kananan hukumomin Furfore da Jada.
Dan sintirin ya shaidawa majiyar mu cewar kauyukan yankin na fama da satar mutane tare da sanar da cewar tuni 'yan kungiyar su ta sintiri ta fara aikinta na tsare lafiya da dukiyar jama'a.
DUBA WANNA: Karya ta kare: An cafke wasu 'yan kungiyar asiri suna tsaka da gudanar da taro da talatainin dare
Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, Othman Abubakar, ya tabbatar da faruwar al'amarin, sannan ya ce suna gudanar da bincike.
"An sanar da mu afkuwar lamarin, saidai bamu samu karin bayanai ba ya zuwa yanzu. Tun kafin yanzu mun san akwai matsalar satar mutane a yankin kuma muna daukan matakan tabbatar da tsaro a wuraren da abin ya shafa", inji Abubakar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng