Hotunan wani katafaren kamfanin jihar Sokoto na noman shanu da babu irinsa Afrika

Hotunan wani katafaren kamfanin jihar Sokoto na noman shanu da babu irinsa Afrika

- Gwamnatin jihar Sokoto ta ce tana daf da kaddamar da wani katafaren kamfanin noman shanu da babu irinsa a Afrika

- Kamfanin zai samar da sabuwar kimiyyar kiwon shanu da kifi da kuma kulawa da dabbobi

- Gwamnatin jihar ta ce katafaren kamfanin da ta gada daga wajen tsohuwar gwamnatin jihar, ya lakume mata biliyan N2.8b

Gwamnatin jihar Sokoto ta ce tana daf da kaddamar da wani katafaren kamfanin noman shanu da babu kamar sa a fadin Afrika ta yamma.

Da yake nuna ginin katafaren ginin ga manema labarai, kwamishinan kula da lafiyar dabbobi da inganta noman kifi, Alhaji Tukur Alkali, ya ce kamfanin zai mayar da hankali ne wajen inganta irin nau'in shanu da muke da su a gida Najeriya tare da samar da sabbin hanyoyin kimiyyar noman dabbobin gida.

Hotunan wani katafaren kamfanin jihar Sokoto na noman shanu da babu irinsa Afrika
Katafaren kamfanin jihar Sokoto na noman shanu da babu irinsa Afrika

Kamfanin dake unguwar Rabah GRA a garin Sokoto, ya lashewa gwamnatin jihar naira biliyan N2.8b, a cewar Alkai. Kazalika ya ce gwamnatin jihar ta gaji aikin ginin kamfanin ne daga tsohuwar gwamnatin jihar.

DUBA WANNAN: Gwamna Tambuwal ya kaddamar da fara sayar da takin gargajiya da aka sarrafa a jihar Sokoto

Da yake karin bayani a kan adadin kudin da kamfani ya lashe, Alkali ya ce gwamnatin jihar ta kashe biliyan N1.5 wajen sayen wasu nau'in shanu na musamman daga kasar Ajantina, gine-gine, bayar da horo ga ma'aikata, tsaro, da kuma zirga-zirga, yayin da yace an kashe biliyan N1.3b domin sayen kayan aikin kamfanin.

Hotunan wani katafaren kamfanin jihar Sokoto na noman shanu da babu irinsa Afrika
katafaren kamfanin jihar Sokoto na noman shanu da babu irinsa Afrika

Alkali ya kara da cewar gwamnatin jihar ta ware wani sashe na musamman a cikin kamfanin da shanu za su ke kiwo.

A shekarar 2010 ne gwamnatin jihar Sokoto ta shiga wata yarjejeniya da wani kamfanin kasar Ajantina (SABT) domin gina kamfani da zai bunkasa kiwon shanu domin madara da nama.

Bisa ga yarjejeniyar, kamfanin SABT zai bayar da horo da kuma samar da irin shanu na musamman da kuma injina da za ai aiki da su a kamfanin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng