Labari mai dadi: Wani babban dan siyasar Jamus ya karbi addinin Musulunci
Rahotanni dake zuwa mana sun nuna cewa mataimakin shugaban jam’iyyar AfD ta 'yan mazan jiya na jihar Brandenburg dake kasar Jamus Arthur Wagner ya karbi addinin Musulunci.
Sahafin jaridar Tagesspiegel ta ruwaito cewa, ba da jima wa ba Wagner ya Musulunta.
An sanar da cewa Wagner ya ki ya yi dogon bayani game da karbar addinin Musuluncin nasa inda ya ce, hakan abu ne da shi ya shafa.
Shugaban Majalisar Shura ta jam'iyyar AfD Andreas Kalbitz ya tabbatar da al’amarin na musuluntar Wagner.
KU KARANTA KUMA: Dandalin Kannywood: Abida Muhammad za ta yi aure a ranar Juma'a mai zuwa
Ya kuma kara da cewa a ranar 11 ga watan Janairu ne Wagner ya sanar da ficewar sa daga majalisar gudanarwar jam'iyyar AfD a jihar Brandenburg.
Kakakin jam'iyyar na jihar daniel Friese ya ce, zabin mutane ne su shiga addinin da suke so.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng