Kalli irin tarbar da Gwamna Fayose ya yi Atiku a garin Ekiti
- Tsohon mataimakin shiugaban kasa Atiku Abubakar zai gana da wasu mambobin jam'iyyar PDP a birnin Ado-Ekiti
- Akwai kishin-kishin na cewa jam'iyyar ta PDP ta zabi 'yan takara 6 da za'a cire dan takarar shugaban kasa daga cikin su
A ranar Laraba 24 ga watan Janairu, Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ziyarci Gwamna Ayodele Fayose na jihar Ekiti.
Hadimin Atiku kan fannin yada labarai, Lere Olayinka ya bayyana cewa Atiku zai gana da wasu zababun yan jam'iyyar ta People's Democratic Party (PDP) a garin Ado-Ekiti.
KU KARANTA: Wata jiha a Kenya za ta yi gwanjon shanu da ke shigowa daga kasar Tanzania
Masoya Gwamna Fayose sun fito kwan su da kwarkwata domin maraba da tsohon mataimakin shugaban kasar yayin da ya sauka a filin jirgi na garin Ado-Ekiti.
Ga wasu daga cikin hotunan irin tarbar da aka yi ma sa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng