Hukumar NDLEA ta bankado wiwi na N20m a Jihar Edo
- Hukumar Yaki da Safaran Muggan Kwayoyi (NDLEA) ta yi kamen wiwi na naira miliyan 20
- Wannan kame ya faru ne a dajin Ugbubezi da ke Karamar Hukumar Owan ta Yamma na Jihar Edo
- Hukumar ta ce babu wani sassauci ko daga kafa sa za ta yi wa ma su safaran kwayoyi
Hukumar Yaki da Safaran Muggan Kwayoyi (NDLEA), ta bankado wiwi na kimanin naira miliyan 20 a wani maboya da ke Dajin Ugbubezi na Karamar Hukumar Owan ta Yamma ta Jihar Edo.
Kwamandan Hukumar na Jihar, Mista Buba Wakawa, shi ne ya bayyana hakan ga manema labarai a yau Laraba a Babban Birnin Jihar, Benin. Ya kuma ce an kama mutane 2 wanda a halin yanzun a ke ma su tambayoyi.
KU KARANTA: Majalisar Dattawa ta shiga cikin maganar zargin da Hukumar Soji ta yi wa wani soja na cewar shi dan Boko Haram ne
Wadanda a ka kaman wanda a da manoma ne, sun alakanta shigar su harkar sana'ar wiwi da bakin talauci. A halin yanzun su na jiran gurgana a gaban kotu.
Wakawa ya bayyana cewar za su iya fuskantar gidan yari na shekaru 15. Ya kuma bayyana cewan babu wani mafaka ko wuri da masu safaran za su buya face Hukumar ta yi ram da su.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng