Babban sufeta janar ya raba ma Yansandan jihar Kano Babura 500

Babban sufeta janar ya raba ma Yansandan jihar Kano Babura 500

Akalla jami’an rundunar Yansandan Najeriya su 500 ne suka ci gajiyar tallafin Babura 500 da babban sufeta janar na kasa, Ibrahim Idris ya raba a jihar Kano, inji rahoton Daily Trust.

Tsarin rabon Babura zai zagaye dukkanin jihohin Najeriya 36, kuma an bullo da shi ne do sauwaka ma Yansanda gudanar da aikace aikacensu na yau da kullum, wanda Katukan Kano, Hakimin Albasu Bashir Abdullahi ya raba, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.

KU KARANTA: Jami’a za ta hukunta duk ɗalibin da ya zazzago da wandonsa, da masu askin banza

Mataimakin Sufetan Yansanda, sashi na 1, AIG Dan Bature ya bayyana tallafin a matsayin manuniya ga irin jajircewa da babban sufetan Yansandan ke nunawa game da walwalar jami’an rundunar, ya bukaci wadanda suka samu Baburan da su dage wajen aikinsu.

Babban sufeta janar ya raba ma Yansandan jihar Kano Babura 500
Babura 500

“Wadannan su ne rukuni na farko da muka raba ma Inspekta da sauran kurata, don haka ake bukatar duk wanda suka ci gajiyar baburan nan da su jajirce a bakin aikinsu domin hakan ya kara ma IG kwarin gwiwar cigaba da samar da kayan aiki rundunar.

“Ina kira ga Yansanda da su dinga kula da hakkokin bil adama, su kasance masu kyakyyawar mu’amala tsakaninsu da fararen hula, don kulla dangantaka mai aminci a tsakaninsu.” Inji Dan Bature.

A nasa jawabin, Kwamishinan Yansandan jihar, Rabiu Yusuf ya gargadi wadanda suka rabauta daga Babura da su guji siyar da su, don duk wanda aka kama ya siyar zai dandana kudarsa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: