Waiwaye: Duk wanda Obasanjo ya marawa baya sai da ya samu mulki a Najeriya
Wani nazari da NAIJ tayi ya nuna cewa tsohon Shugaba kasa Janar Olusegun Obasanjo bai taba goyon bayan wanda bai kai labari ba haka kuma wadanda su kayi adawa da shi kan sha kashi. Wannan karo yayi kaca-kaca da APC da PDP.
Tarihi ya nuna cewa ba a taba kada tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo a harkar siyasa ba a tarihin Najeriya tun daga lokacin juyin mulki har ila yau. Wannan karo dai ya nemi Shugaba Buhari ya hakura da mulki.
Tarihi ya nuna cewa Olusegun Obasanjo wanda yayi mulkin Soja har zuwa 1979 ya san da duk juyin mulkin da aka yi a Kasar wanda har ta sa aka daure sa bisa zargin kifar da Gwamnatin Janar Sani Abacha bayan yayi ritaya.
KU KARANTA: Inda Shugaban kasa Buhari yayi kuskure - Obasanjo
Janar Olusegun Obasanjo ya dawo mulki lokacin farar hula daga 1999 zuwa 2007. Bayan nan kuma ya marawa Marigayi Ummaru 'Yaradua wanda ya kara kada Janar Muhammadu Buhari wanda ya rasu a kan mulkin Kasar.
Bayan rasuwar 'Yaradua, Obasanjo ya goyi bayan Goodluck Jonathan na PDP kafin abubuwa su cabe tsakanin su. Daga nan ne kuma tsohon Shugaban kasar ya marasa Jam'iyyar APC ta Shugaba Buhari baya a 2014.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng