Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da yara bakawai da kashe mutane tara a jihar Adamawa
- 'Yan bindiga sun kai wa wani kauye a jihar Adamwa hari a ranar Talata
- Kungiyar 'yan banga sun fara farautar 'yan bindigan da suka yi awon gaba da yara bakwai a kauyen Iware
Wasu ‘yan bindiga sun kai wa kauyen Iware dake kan hanyar Fufore zuwa Jada a jihar Adamawa hari a ranar Talata.
‘Yansanda da mazauna garin sun ce ‘yan bindigan sun kashe mutane tara, da sace yara guda bakawai.
Wani danbanga yace, ‘yan mata da ake zargin ‘yan ta’adda ne suka kawo wa kauyen su hari a cikin dare, suka kashe mutane tara a cikin daga gida daya.
‘Yan ta’adda sun sace yara guda bakwai a kauyen, kuma yanzu suna tambaya kudin fansa ran su.
“Mun sanar da jami’an tsaro da gwamnati akan wannan al'amari, kuma kungiyar mu na ‘yan banga sun fara farautar masu laifin dan kama su,” inji dan banga.
KU KARANTA : Fayose yayi kaca-kaca da Obasanjo akan budaddiyar wasikar da ya rubutawa Buhari
Mai magana da yawun bakin rundunar ‘yansandar jihar Adamawa, SP Othman Abubakar, ya tabbatar da aukuwan wannan lamari kuma ya ce jami’an su sun fara bincike.
A shekara da ta gabata masu garkuwa da mutane suka sace wani attajirin dan kasuwa da dan majalissar dokoki na jihar Adamawa mai wakiltar mazabar Toungo .
A cikin kwanaki 'yan kadan da suka gabata aka kara yin awon gaba da dan uwan tsohon shugaban hukumar EFCC Nuhu Ribadu, mai suna Sani Ribadu.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng