Dole a cire Nikabi a ofishin mu inji Kwansul Janar na Saudi
- Wani babban Malami ya kira Jakadun Najeriya a Jeddah kasar Saudiyya
- Gumi ya nemi a sake dokar hana mata sa nikabi a ofishin Jakadancin kasar
- Babban Malamin ya nemi hukuma su ji tsoron Allah a ba kowa hakkin sa
Legit.ng ta samu labari na musaman cewa babban Malamin Addinin Musulunci Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya soki tsarin haramtawa Mata daga Najeriya Nikabi a ofishin Jakadancin Najeriya a Kasar Saudiyya.
Idan ba a manta ba kwanan nan ofishin bada biza da sauran takardun shiga Kasar Saudiyya ta haramtawa Mata shiga neman biza da fuskar su a rufe. Sheikh Ahmad Mamud Gumi ya kira Ambasada Muhammad Sani Yunus a wayar tarho.
KU KARANTA: Rikicin Makiyaya ya dame ni - Shugaba Buhari
Kwansal Janar na kasar yace ba zai cire wannan doka ba inda yace duk wanda ba zai bi wannan ka’ida ba ya hakura da neman biza a lokacin da ya zanta da Malamin a wayar salula. Shehin Malamin da yace sam bai dace a tauye hakkin kowa ba.
Babban Malamin ya nemi jin dalilin ya sa aka kafa wannan doka tun da ‘Yan kasa na da hakkin shiga yadda su ke so. Sai dai Kwansul din kasar Sani Yunusa ya tubure ya fadawa babban Malamin babu wanda ya isa ya shiga cikin aikin sa.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng