Wata jiha a Kenya za ta yi gwanjon shanu da ke shigowa daga kasar Tanzania

Wata jiha a Kenya za ta yi gwanjon shanu da ke shigowa daga kasar Tanzania

- Za a yi gwanjon shanaye 'yan Tanzaniya da su ke gararamba a Babban Birnin Kenya

- Mai Gudanar da Harkokin Noma na Birnin, Denvas Makori, shi ne ya bayyana hakan

- Ya ce makiyayan su na kiwo cikin birnin ne ba tare da izinin gwamnati ba

- A cewar wasu kuwa, kamen shanayen mayar da martani ne ga yadda Tanzaniya ta yi wa makiyayan Kenya

Majalisar Dokoki na Babban Birnin Kenya ta kudiri aniyar yin gwanjon shanaye da su ke gararamba cikin birnin. Mai Gudanar da Harkokin Noma, Danvas Makori, shi ne ya bayyana hakan ga Jaridar Star.

Ya ce duk da kasancewar wasu daga cikin shanayen daga Kajiado da Narok su ke, amma akasarin su daga Tanzaniya su ke. A cewar sa, doka ta hana yin kiwo a birnin ba tare da izini gwamnati ba.

Wata jiha a Kenya za ta yi gwanjon shanu da ke shigowa daga kasar Tanzania
Wata jiha a Kenya za ta yi gwanjon shanu da ke shigowa daga kasar Tanzania

Denvas ya kuma ce ba a da masaniyar irin cututtukan da shanayen ke dauke da su. Bisa wadannan dalilai ne za a yi gwanjon na su, in ji shi.

DUBA WANNAN: Wani Jauro ya kama 'dan fashi da ke kokarin far ma kurkuku da hari

Sai dai kuma wadansu su na zargin za a yi gwanjon shanayen ne don mayar da martani ga kamen shanayen 'yan Kenya da Kasar Tanzaniya ta yi a watar Disamba na 2017, a inda ta kama fiye da shanaye 1300 har sai da a ka yi belin kowanne kan Sh5000.

Sai dai shi kuma Denvas ya ce fafutukar neman ruwa da ciyawa da kuma kasuwar nono shi ya sa makiyayan ke shigowa cikin birnin, hakan kuwa doka ta hana. Ya kuma ce Sh5,000 ya yi kadan ga beli, don haka za su daga na su kudin belin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164