Gwamnatin jihar Kebbi za ta magance faruwar rikicin makiyaya ta wata hanya ta musamman

Gwamnatin jihar Kebbi za ta magance faruwar rikicin makiyaya ta wata hanya ta musamman

- Gwamnatin jihar Kebbi za ta gina gidaje 1,000 domin makiyaya

- Gwamnatin jihar ta ce yin hakan zai kiyaye afkuwar tashe-tashen hankula tsakanin makiyaya da manoma a jihar

- Gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Bagudu, ne ya sanar da hakan

Gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Bagudu, a jiya Talata, ya ce gwamnatinsa ta fara wani shirin gina muhalli 1,000 domin makiyaya. Gwamnan ya ce jihar za ta yi hakan ne domin kiyaye afkuwar rigingimun makiyaya da manoma a jihar.

Gwamnatin jihar Kebbi za ta magance faruwar rikicin makiyaya ta wata hanya ta musamman
Gwamnatin jihar Kebbi za ta magance faruwar rikicin makiyaya ta wata hanya ta musamman

Bagudu ya bayyana haka ne yayin gabatar da kasafin kudi, biliyan N151b, na shekarar 2018.

Ya ce za su samar da ruwa, abincin dabbobi, da sauran kayayyaki a muhallin makiyayan.

DUBA WANNAN: Wani Jauro ya kama 'dan fashi da ke kokarin far ma kurkuku da hari

Ya kara da cewar, babban abinda ke jawo rikici tsakanin makiyaya da manoma, batu ne na kasa da albarkatunta.

Bagudu ya ce samar da muhalli dake da dukkan abinda makiyaya ke bukata, zai hana afkuwar rikici tsakaninsu da manoma.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewar gwamna Bagudu ya bayar da tabbacin raya tare da bunkasa harkar noman kifi a jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng