Wurin kiyo: Sanata daga jihar Kaduna ya tozarta shugaba Buhari
Sanatan dake wakiltar jihar Kaduna ta kudu a majalisar dattijan Najeriya watau Sanata Danjuma Laah a jiya Talata ya yi fatali da kiran gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari na kebe wuraren kiwo na musamman domin fulani a yankin.
Sai dai Sanatan ya bayyana cewa yankin da yake wakilta ko kusa ba za su taba amincewa da hakan ba domin kuwa dukkan kasar dake yankin su suna anfani da ita ne wajen noma kuma ba za su taba baiwa wasu bakin haure ba.
KU KARANTA: Gwamnatocin tarayya, jahohi sun raba Naira 655 biliyan a Janairu
Legit.ng dai ta samu cewa a 'yan kwanakin nan dai an samu tashe-tashe hankula sosai musamman ma tsakanin manoma da makiyaya jahohin dake arewa ta tsakiyar Najeriya da kuma ma sauran sassan Najeriya batun da yayi matukar daukar hankalin 'yan Najeriya.
A wani labarin kuma Kwamitin dake yin duba game da yadda ake kasafta dukiyar kasa watau Federation Account Allocation Committee (FAAC) a turance a jiya Talata ya sanar da kasafta Naira 655 biliyan a tsakanin gwamnatocin tarayya, jahohi da kuma kananan hukumomi a watan nan na Janairu.
Da take karin haske game da lamarin, ministar kudi ta gwamnatin tarayyar Uwar gida Kemi Adeosun ta bayyana yadda aka yi kason da kuma daga inda aka samu jimmillar kudaden da har su ka kai yawan hakan.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
Asali: Legit.ng