Zazzaɓin Lassa: Gwamnatin jihar Anambra ta haramta shan garri
Gwamnatin jihar Anambra ta sanya dokar haramta shan garri a jihar a matsayin mataki na hana yaduwar cutar zazzabin Lassa.
Kwamishinan lafiya na jihar, Dakta Joe Akabuike, shine ya sanar da dokar a yayin da yake wayar da kai tare ilmantar da mazauna jihar akan matakan kare cutar wadda ke ci gaba da yaɗuwa a wasu sassa na kasar nan.
Dakta Joe ya kirayi ɗaukacin al'ummar jihar sa a kan su faɗaku wajen kiyaye dukkan hanyoyin tsaftacewa tare da kula da muhallansu, jikinsu da kuma musamman abincin su da na shan su domin ita kaɗai ce hanyar dakile cutar daga yaɗuwa.
KARANTA KUMA: Wani ɗan shekara 30 ya gurfana da laifin lalube a budurcin ƙaramar yarinya
A ranar talatar da ta gabata ne kuma, likitoci na jihar Kogi suka gudanar da taro a birnin Lokoja domin ta'aziyar wani abokin su da ya riga mu gidan gaskiya a sanadiyar cutar ta Lassa a ranar lahadin da ta gabata.
Legit.ng ta ruwaito cewa, Dakta Ahmed ɗan shekara 30 ya cika ne a garin Irrua na jihar Edo, a yayin da yake duban lafiyar wani jariri mai ɗauke da cutar wanda tuni shima ya riga mu gidan gaskiya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng