Wani Jauro ya kama 'dan fashi da ke kokarin far ma kurkuku da hari

Wani Jauro ya kama 'dan fashi da ke kokarin far ma kurkuku da hari

- Wannan lamari ya faru ne a Jihar Delta a inda dan ta'addan ya yi niyyar fasa gidan yari da ke Ogwashi na Jihar

- An kama dan ta'adda dauke da muggan sindarai wanda ya bayyana cewan bom ne da ya yi niyyar fasa gidan yarin da shi

- Kwamishinan 'Yan Sanda na Jihar, Muhammad Alhaji Mustapha, ya tabbatar da faruwar wannan kame

A ranar Talata ne Hukumar 'Yan Sandan Jihar Delta su ka bayyana wani dan ta'adda da a ka kama da kudirin fasa gidan yari da ke Ogwashi. Wani matashin Bafillatani Makiyayi, Sani Ibrahim, mai shekaru 18 wanda ke zaune a sansanin Fulani na Ogwashi-Uku, shi ne ya kama dan ta'addan.

Wani Jauro ya kama 'dan fashi da ke kokarin far ma kurkuku da hari
Wani Jauro ya kama 'dan fashi da ke kokarin far ma kurkuku da hari

Dan ta'addan mai suna Sekemiya Fullpower, dan garin Yokoromor, Karamar Hujumar Burutu ta Jihar Delta, ya shaidawa manema labarai bayan an kama shi cewan ya yi kudirin fasa gidan yarin ne don tseratar da abokan barnar sa da su ke tsare a gidan yarin.

KU KARANTA: Dalilin da ya sa har yanzun ba a ladabatar da kowa ba game da mayar da Maina bakin aiki - Oyo-Ita

Sabon Kwamishinan 'Yan Sanda na Jihar, Muhammad Alhaji Mustapha, ya bayyana cewan sakamakon rashin natsuwa da kamanni da yanayi na Fullpower ya sa Fulani mazauna sansanin su ka kama shi su ka mika shi ga Hukuma.

Fulanin sun kama shi dauke da muggan sindarai wanda ya bayyana cewan bom e wanda da shi ya yi niyyar fasa gidan yarin. Mustapha ya yaba da irin kokarin da Fulanin su ka yi na kama wanann dan ta'adda.

Ya kuma yabawa al'umma game da irin hadin kai da su ke ba Hukuma don gannin an magance ta'addanci. Ya kuma yi kira gare su da su kara bisa kokari da hadin kan na su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164