Gwamna El-Rufai ya raba ma Sarakunan jihar Kaduna motocin alfarma (Hotuna)
Sarakunan jihar Kaduna masu daraja ta uku sun samu tagomashin manyan motoci daga gwamnatin jihar Kaduna a ranar Talata 23 ga watan Janairu, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.
Sarkin Zazzau, kuma shugaban sarakunan gargakiya na Kaduna, Alhaji Dakta Shehu Idris ne ya mika wadannan motoci ga Sarakunan su 13 a wani karamin biki daya gudana a gidan gwamnatin jihar Kaduna.
KU KARANTA: Tattakin siyasa: Masoya Kwankwaso su 2 sun durfafi jihar Kano tun daga Kaduna a ƙasa
Motocin na alfarma, Samfurin Pijo 301, an raba su ne ga Sarakunan don taimaka musu wajen gudanar da sha’anin mulki cikin sauki.
Da yake jawabi a yayin mika Motocin, gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufai ya bayyana cewa ya lura wasu Sarakuna na yawo ne cikin motocin haya, don haka ne gwamnati ta yanke shawarar siya musu motoci.
Daga cikin Sarakunan da suka samu wannan Motoci akwai na Saminaka, Kumana, Godogodo, Kaninkon, Fantswan, Nyenka, Kurama, Piriga, Tsam,Takad, Ayu, Ikulu da Anghan
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng