Tattakin siyasa: Masoya Kwankwaso su 2 sun durfafi jihar Kano tun daga Kaduna a ƙasa

Tattakin siyasa: Masoya Kwankwaso su 2 sun durfafi jihar Kano tun daga Kaduna a ƙasa

- Wasu Kwankwasawa guda biyu sun kama hanyar Kano daga Kaduna a kasa

- Magoya bayan Kwankwason sun tafi ne domin tarbarsa a ziyarar da zai kai jihar

Wasu masoya kuma magoya bayan tsohon gwamnan jihar Kano,Sanata Rabiu Musa Kwankwaso sun nufi jihar Kano a kasa, daga jihar Kaduna, don samu halartar taron ziyarar da gwanin nasu zai kai a ranar 30 ga wata.

Wani jigo a tafiyar Kwankwasiyya, kuma ma’bocin kafar sadarwar zamani ta Facebook, Sani Saeed Altukry ne ya bayyana haka, bayan ya samu damar raka wadannan Kwankwasawa guda, biyu, tare da daura hotunansu.

KU KARANTA:Bambarakwai: Sabuwar Amarya ta kashe jaririyarta kwana guda da haihuwa

Tattakin siyasa: Masoya Kwankwaso su 2 sun durfafi jihar Kano tun daga Kaduna a ƙasa
Bashir

Majiyar Legit.ng ya bayyana sunayen mabiya kwankwasiyyan kamar haka: Usman Lawal Bari da Bashir Abubakar, kuma sun yi shirya wannan tattaki ne don tarbar Mahadin Kwankwasiyya, Rabiu Kwankwaso tare da jaddada goyon baya a gare shi.

Daga karshe sun bukaci jama’a su taya su da addu’a don sauka lafiya

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: