Saukar makamai jihar Taraba: Karya ne, babu makaman da ya sauka – Hukumar yan sanda

Saukar makamai jihar Taraba: Karya ne, babu makaman da ya sauka – Hukumar yan sanda

- Hankalin jama'a ya tashi ranan Asabar bisa ga labarin cewa jirgi ya kawo makamai kauyen Jibu

- Gwamnatin jihar ta ce an kawo su ne domin kashe mutanen jihar

- Amma hukumar yan sandan jihar ta karyata wannan labari

Hukumar yan sandan jihar Taraba a ranan Talata ta yi Allah wadai da ikirarin gwamnatin jihar Taraba cewa wani jirgi mai saukan angulu dauke da makami ya sauka kauyen Jibu da ke karamar hukumar Wukari, jihar Taraba, ranan Asabar.

Kwamishanan yan sandan jihar, Mr. Dave Akinremi, a wata hira da manema labarai a Jalingo yace wannan labari karya ne, yaudara ne kuma ana son tayar da hankalin jama’a ne kawai.

Saukar makamai jihar Taraba: Karya ne, babu makaman da ya sauka – Hukumar yan sanda
Saukar makamai jihar Taraba: Karya ne, babu makaman da ya sauka – Hukumar yan sanda

Amma, mai magana da yawun gwamnan jihar jihar, Mr. Bala Dan-Abu, ya jaddada cewa lallai an sauke makamai jihar.

KARANTA WANNAN: Reuben Abadi ya sami damar yabon uwargidan shugaba Buhari Aishatu

“Muna da majiyoyin labaranmu, kuma ina tabbatar muku da cewa jirgi mai saukan angulu ya sauka kauyen nan da makamai. Mun samu labarinmu ne daga majiya mai karfi. Kawai yan sanda suyi bincike mai zurfi domin tsare mutanen Taraba.”

Kwamishanan yan sandan jihar y ace shi da kansa ya garzaya kauyen domin tabbatar da sihhancin labarin amma duk karya ne.

Saukar da sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu ta wannan link din: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: