Wani ɗan shekara 30 ya gurfana da laifin lalube a budurcin ƙaramar yarinya

Wani ɗan shekara 30 ya gurfana da laifin lalube a budurcin ƙaramar yarinya

A ranar talatar da ta gabata ne, wani ɗan shekara 30 Lamidi Alabi, ya gurfana a gaban kotun majistire ta Ebute Meta, da laifin sanya hannu tare da shafar gaban wata ƙaramar yarinya 'yar shekara bakwai a jihar Legas.

Alabi ya gurfana a gaban kotun da laifin cin zarafi tare da keta haddin ƙaramar yarinya, sai dai kotun ba ta kama shi da aikata laifin tuhumar da ake yi akan sa ba.

Jami'ar 'yan sanda, Sajen Kehinde Omisakin, ta shaidawa kotun cewa Alabi ya aikata wannan laifi ne da misalin ƙarfe 11:58 na ranar 21 ga watan Janairu a hanyar Ebute Meta ta jihar Legas.

Jami'an 'yan sanda
Jami'an 'yan sanda

Omisakin ta ci gaba da cewa, mutane masu bibiyar hanyar ne suka damƙo Alabi a yayin da yake yunƙurin samun damar afkawa wannan yarinya.

KARANTA KUMA: Wani ɗan kasuwa ya keta haddin 'yar riƙon sa a jihar Legas

Ta ƙara da cewa, wannan laifi ya sabawa sashe na 135 na kundin tsarin dokokin jihar Legas.

Alƙalin kotun, mai shari'a Tajudeen Elias, ya ɗaga sauraron ƙarar zuwa ranar 29 ga watan Janairu ba tare da bayar da belin wanda ake tuhuma ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng