Yan sanda sun gurfanar da mai yiwa Buhari yakin neman zabe karo na biyu bayan ya caccaki hadiman shugaban kasa

Yan sanda sun gurfanar da mai yiwa Buhari yakin neman zabe karo na biyu bayan ya caccaki hadiman shugaban kasa

- Yan sanda sun gurfanar da Alhaji Dan’Bilki Komanda a jihar Kano bayan wani korafi daga hadiman shugaban kasa Muhammadu Buhari guda biyu

- An gurfanar da shi a gaban kotun majistare na 26 a Kano kan laifin satar kammanin wani

- Korafin ya biyo bayan wani hari da ya kai ma hadiman shugaban kasa

An gurfanar da wani mai ikirarin yakin neman ma Shugaban kasa Muhammadu Buhari zabe karo na biyu a kotun majistiri na 26 a Kano akan laifin zamba.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, mai yakin neman zaben ya kasance sanye da riga mai tsawo tare da hula, ya gurfana a kotu ne bayan an fidda shi daga kurkukun yan sanda tare da tsaurarriyar tsaro.

Yan sanda sun gurfanar da mai yiwa Buhari yakin neman zabe karo na biyu bayan ya caccaki hadiman shugaban kasa
Yan sanda sun gurfanar da mai yiwa Buhari yakin neman zabe karo na biyu bayan ya caccaki hadiman shugaban kasa

Komanda ya fada a matsala ne bayan wani kara da wasu mataimaka na musamman ga shugaban kasa Buhari, Sha’aban Sharada, Bashir Suleiman da wani abokinsu, Malam Hafiz suka mikawa yan sanda don bincikan mabayyannin yakin neman zabe ga shugaban kasa Muhammadu Buhari saboda “harinsu da yayi a wani shiri da aka gabatar a gidan radiyo a Kano.

KU KARANTA KUMA: Allah ya kyauta! Kannen miji sun hallaka matar yayansu a Katsina

Kokari da wani jami’in dan sanda yayi don ganin ya dauki Dan Bilki hoto a matsayar jirgin ruwa ya janyo rikici tsakanin yaransa kafin jami’an tsaro su sassauta al’amarin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: