Bala Lau ya zama shugaban kungiyar Izala ta nahiyar Turai

Bala Lau ya zama shugaban kungiyar Izala ta nahiyar Turai

- Bala Lau shi ne shugaban kungiyar Izala ta Najeriya

- Kungiyar Izala ta nahiyar Turai ta nada shi shugabanta

- An ginawa kungiyar Ofis

Shugaban kungiyar Izalatul-Bid'a-Wa-Iqamatus-Sunnah da aka fi sani da Izala, Bala Lau, ya zama sabon shugaban kungiyar Izala ta nahiyar Turai bakidaya. Kungiyar Izala reshen Turai, ta gayyaci Lau kuma bayan ya amsa gayyatar ta nada shi shugabanta.

Bayan nadin na shi, wata kungiya (Sautus Sunnah), ita ma dake can Turai din, ta ginawa kungiyar Izala ta Turai Ofis.

Bala Lau ya zama shugaban kungiyar Izala ta nahiyar Turai
Bala Lau ya zama shugaban kungiyar Izala ta nahiyar Turai

Majiyar mu ba ta sanar da mu ko Sheikh Bala Lau ne zai amfani da Ofishin ba.

KU KARANTA: Ya yi wuri a fara zargin kungiyar ISIS da hannu a cikin rigingimun makiyaya - Hukumar 'yan sanda

Da kungiyar ke tabbatar da Sheikh Lau a matsayin shugabanta, kakakin kungiyar ya ce "munyi nazarin kungiyoyin Izala fiye da 60 a duniya. Ba mu samu wata kungiyar Izala da cikin kankanin ta samu cigaba ba, kamar ta Najeriya. Kuma hakan ne ya saka mu ka gayyace ka domin ba ka ragamar ta mu kungiyar."

A kwanakin baya ne dai Sheikh Bala Lau da Sheikh Kabiru Gombe su ka yi tattaki ya zuwa Turai domin gabatar da wa'azi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng