Sakin Zakzaky ba zai hana gwamnati daukaka kara ba – Inji Kotu

Sakin Zakzaky ba zai hana gwamnati daukaka kara ba – Inji Kotu

- Kotun daukaka kara ta fara sauraron karar da gwamnatin tarayya ta daukakka kan hukuncin da wata babban kotu ta yanke kan Zakzaky

- Kotun ta nuna rashin jindadi ga kin bin hukuncin kotu da gwamnatin tarayya tayi na ta saki Zakzaky

- Kotun ta ce sakin Zakzaky ba zai hana gwamnatin tarayya daukaka kara ba

Rahotanni sun kawo cewa a yau Litinin, 23 ga watan Janairu ne kotun daukaka kara a Najeriya ta fara sauraron karar da gwamnatin tarayya ta daukaka, akan hukuncin da wata babbar kotun kasar ta bayar da umurnin a saki shugaban kungiyar Shi’a, Ibrahim El-Zakzaky.

Alkalai uku ne suka saurari karar da gwamnatin tarayya ta daukaka a yau.

Mai shari'a Mojeed Owoade wanda ya jagoranci zaman kotun da kuma mai shari'a Chidiebere Uwa sun nuna rashin jin dadinsu kan yadda gwamnati ta ki mutunta hukuncin kotun kasar, abin da suka ce bai da ce ba.

Sakin Zakzaky ba zai hana gwamnati daukaka kara ba – Inji Kotu
Sakin Zakzaky ba zai hana gwamnati daukaka kara ba – Inji Kotu

Alkalan sun jadadda cewa sakin El Zakzaki ba zai hana gwamnati ta daukaka karar da ta ke akan sa ba.

KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari zai sha kashi a zabe 2019 – Ahmed Makarfi

A shari'ar da aka fara saurare dai, shugaban kungiyar na Shi'a Ibrahim El-Zakzaki bai samu damar halartar kotu ba.

Haka zalika kotun ba ta tsayar da takamammiyar ranar da zata ci gaba da sauraren karar ba.

A baya Legit.ng ta ruwaito cewa Daruruwan mata yan akidar Shi'a sun gudanar zanga-zanga yau a Abuja, domin kira ga gwamnatin tarayya kan a saki Sheikh Ibrahim Zakzaky.

Matan kungiyar sun gudanar da jerin gwanon ne bayan anyi artabu da wasu matasan kungiyar da sukayi irin wannan zangan-zangan a babban birnin tarayya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng