Za mu iya lashe zaben 2019 – inji Shugaban Jam’iyyar adawa Accord
- Jam’iyyar adawa ta Accord ta ce ta na sa ran lashe zaben shekarar 2019
- Jam’iyyar yace ba su da niyyar hada karfi-da karfi da sauran Jam’iyyu
- Shugaban Jam’iyyar yace yanzu Jam’iyyar Accord ta kawo karfi a kasar
Mun samu labari daga Jaridar Daily Trust ta kasar nan cewa Jam’iyyar adawa ta Accord na neman wanda zai yi takarar kujerar Shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar a zabe mai zuwa na 2019.
Jam’iyyar adawar tana neman wanda ya cacanci daga tutar Jam’iyyar a zaben 2019. Sai dai Jam’iyyar adawar tace ba ta da niyyar hada kai da sauran Jam’iyyu a zaben. Shugaban Jam’iyyar Mohammed Lawal Nalado ya bayyana wannan.
KU KARANTA: Inyamuran Najeriya za su goyi bayan Shugaba Buhari
Shugaban Jam’iyyar ta Accord wanda kuma shi ne Shugaban Majalisar Jam’iyyun siyasa na kasar watau IPAC yace za su iya lashe zabe a kasar a shekarar 2019. Nalado yana ganin yanzu Jam’iyyar sa ta rika ta kara karfi a siyasar Najeriya.
Lawal Nalado bayan yace ba za su shiga wata yarjejeniya da sauran Jam’iyyun adawa ba, ya kuma tabbatar da cewa zaben 2019 zai masu kyau fiye da sauran wadanda aka yi a baya don kuwa yanzu sun shiga ko ina a kasar an san su.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng