Yanzu Yanzu: Tsohon Alkalin Alkalai na Kasa, Dahiru Musdapher ya rasu
Mun samu labarin rasuwar tsohon Alkalin Alkalan Najeriya, Dahiru Musdapher, Mista Musdapher mai shekaru 75 a duniya ya rasu ne a daren jiya.
Kanin marigayin, mai suna Muneer Mustapha ne ya bayar da sanarwan rasuwar ta dandalin sada zumunta na Facebook. A halin yanzu ba'a bayyana abin da yayi sanadiyar rasuwar ta sa ba.
KU KARANTA: Rikicin Makiyaya: An saka dokar takaita fita bayan wani mummunan zang-zanga a garin Zing
Marigayin ya yi retire daga aiki shekaru biyar da suka wuce bayan ya kai shekarun yin murabus. Yana gab da murabus ne tsohon shugaba Jonathan ya nada shi a matsayin Alkalin Alkalai bayan murabus din Alkali Alysious Katsina-Alu, daga baya kuma Alkali Aloma Mariam Mukhtar ta maye gurbin sa.
Marigayin ya yi karatun ne a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria kuma daga bisani ya tafi Jami'ar 'SOAS' da ke garin Landan.
Ya zama Barrista ne a shekarar 1968 kuma yana daya daga cikin wadanda suka fara aikin Lauya masu zaman kansu a kasar nan.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng