Yan sanda sun kama wata mata bayan ta jefar da sabon jaririnta a Jigawa

Yan sanda sun kama wata mata bayan ta jefar da sabon jaririnta a Jigawa

Hukumar yan sandan jihar Jigawa ta kama wata mata mai shekaru 25 da haihuwa, wacce aka rahoto cewa ta jefar da jaririyar da ta haifa a yankin karamar hukumar Guri na jihar.

Mai magana da yawun yan sandan yankin, SP Abdu Jinjiri, ya tabbatar ma kamfanin dillancin labarai al’amarin a Dutse a ranar Litinin.

Jinjiri ya bayyana cewa an zargi mai laifin da jefar da jaririn a ranar 18 ga watan Janairu kusa da wani filin kwallon kafa.

“Wassu yan kwallo ne suka kai rahoto ga hukumar yan sanda kwana biyu bayan ta jefar da jarin a gefen wani filin kwallo.

“Yan kwallon sun kai rahoto ga hukumar yan sanda bayan lura da suka yi da warin gawar jinjirin dake tashi."

Jinjira ya ce “Hukumar yan sanda tayi bincike da kuma kama matar da ta jefar da jaririn da ta haifa”.

Yan sanda sun kama wata mata bayan ta jefar da sabon jaririnta a Jigawa
Yan sanda sun kama wata mata bayan ta jefar da sabon jaririnta a Jigawa

Ya bayyana cewa wacce ake zargin, ta kasance sakakka kuma mazauniyar kauyen Abunabo, ta jefar da jaririn ne bayan ta haife shi watanni hudu bayan sabon aurenta.

Mai magana da yawun hukumar yan sandan ya kara da cewa mai laifin ta kasance da ciki a lokacin da aka aurar da ita ga wani mutum mai shekaru 50.

KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari zai sha kashi a zabe 2019 – Ahmed Makarfi

A cewar shi, mai laifin ta furta cewa wani mai suna Umar Lili, mai shekaru 25 daga kauyewn Musari a yankin karamar hukumar yankin ne yayi mata ciki.

Jinjiri ya ce ana cigaba da gudanar da bincike akan lamarin wanda bayan haka ne za a gurfanar da mai laifin a gaban kotu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng