Wani tsoho mai shekara 120 ya damfari wani Bawan Allah a Jihar Osun
- Ana karar wani mai shekaru 120 a gaban Kotu bisa zargin cin wasu kudi
- Wannan tsoho ya karbi kudi daga hannun wani da sunan saida masa fili
- Yanzu an tashi babu kudin Bawan Allah kuma babu fili tun shekarar 2015
Labari ya zo mana cewa Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya na Jihar Osun sun kama wani tsoho mai shekaru 120 da ake zargi da laifin mallakar wasu makudan kudi ta hanyar da ba ta dace ba.
‘Yan Sandan sun damke PA Busari Oyewumi ne bisa zargin yaudarar wani Bawan Allah mai suna Wasiu Adebisi ya karbe masa kudi har kusan Naira rabin Miliyan. Yanzu haka maganar ta kai gaban Alkalin majitsare Fatima Sodamade.
KU KARANTA: Kungiyar Jama'atul Nasril Islam ta fallasa CAN
Lauyan ‘Yan Sandan Kasar Taiwo Adegoke ya bayyanawa Kotu cewa ana zargin wannan tsohon da yin gaba da N400, 000 na wani mutumi tun a shekarar 2015. Hakan dai ya sabawa dokar kasa na final kwad da kuma Jihar Osun.
Wannan tsoho ya karbi kudin Wasiu Adebisi ne da niyyar zai saida masa fili amma yayi awon gaba da kudin sa. Yanzu haka da Kotu ta bada belin wannan tsoho tukuf, an kuma daga kara har sai zuwa farkon watan Maris mai zuwa.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng