'Yan mata 80 sun tsallake rijiya da baya a jihar Sokoto
- An yi wata mummunar gobara a makarantar sakandiren 'yan mata dake Mabera a jihar Sokoto
- An zargi wutar lantarki da haddasa gobarar
- Ba'a samu asarar rai ba sakamakon gobarar
Dalibai 80 mata sun auna arziki a makarantar sakandiren 'yan mata (GGSS) dake karamar hukumar Mabera a jihar Sokoto bayan da gobara ta babbake dakunansu na kwana a daren jiya, Lahadi.
Kamfanin dillancin labarai (NAN) ya rawaito cewar wutar gobarar ta lalata dakuna hudu na daliban a daya daga cikin dakunan kwanansu, Aisha House.
Rahoton NAN ya ce da kyar jami'an hukumar kashe gobara da hadin gwuiwar ragowar jami'an tsaro su ka kashe wutar gobarar da ake zargin wutar lantarki ce ta haddasa ta.
KU KARANTA: Rushe ofishin jam'iyyar PDP a Maiduguri ya bar baya da kura
Hukumar makarantar ta ki cewa komai a kan batun, su na masu cewar basu da hurumin magana da manema labarai.
Kazalika, kokarin jin ta bakin ma'aikatar ilimin jihar ya gagara. Ba su amsa kiran manema labarai ba, haka kuma ba su dawo da sakon ko ta kwana da aka aike masu ba.
Ko a watan Disamba na shekarar da ta gabata, 2017, saida gobara ta kone dakin kwanan dalibai a makarantar sakandiren kimiyya dake Kware a jihar ta Sokoto.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng