Manoma Timatir a jihar Kano sun yi asara ta naira miliyan dubu daya biyo bayan rufe madatsar ruwan Tiga
Manoman Timatir a jihar Kano sun tafka asarar data kai ta naira biliyan 1, biyo bayan rufe madatsar ruwan Tiga, da hukumar kula da cigaban madatsun ruwan kasar nan ta yi.
Sakataran kungiyar manoma Timatir na kasar, Sani Danladi Yadakwari ya shaida ma kamfanin dillancin labaru, NAN, haka a ranar Litinin 22 ga waran Janairu a garin Kano, ya dangantan hakan ga rufe Tiga Dam.
KU KARANTA: Shuwagabannin APC sun watsa ma Shehu Sani ƙasa a ido: tuggun El-Rufai ne – Inji Sanata
Majiyar Legit.ng ta ruwaito Danladi na fadin cewar madatsar ruwa na Tiga kadai ke samar da ruwa ga manoman jihar gaba daya, don haka, rufe shi ya janyo a asarar kasha 60:
“jihar Kano kadai na samar da tan 400,000 na timatir, amma rufe madatsar ruwan ya kawo nakasun tan 60,000.”
Madatsar ruwan da a yanzu haka ya kai sama da kwanaki 40 a rufe ya janyo nakasun ruwan noma ga manoma da dama, don haka ya bukaci hukumar da madatsun dasu dinga sanar da manoma da sauran masu ruwa da tsaki idan zasu gudanar da aiki a madatsar don kauce ma irin matsalar nan a gaba.
Gonakin da matsalar ta shafa sun hada da Kura, Garunmalam, Bunkure da wasu gonakai a garin Rano, hakan ne ya sanya kungiyar manoman aika ma ministan harkokin noma wasika don neman hanyar shawo kan irinwannan matsala, ya kara da cewa sai da suka fara aikin suka fada musu.
Sai dai Kaakakin hukumar kula da madatsun ruwan Najeriya, Salisu Baba Hamza ya bayyana cewar hukumar ta sanar da shugaban hukumar manoma da ma sakataren kungiyar kafin su fara aiki, baya da sanarwa da suka sanya a gidajen rediyon jihar.
Kaakakin yace “Ana gyaran hanyar fitar ruwa daga madatsar ne, wanda ya rushe a bayan, wanda kuma idna ruwa ya cigaba da bi ta wajen zai janyo lalacewar madatsar ruwan gaba daya. Don haka ba gaskiya bane ace bamu sanar da su ba kafin fara rufe madatsar.”
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng