Dalilin da yasa na sauya sheka zuwa Jam’iyyar APC – Dakingari

Dalilin da yasa na sauya sheka zuwa Jam’iyyar APC – Dakingari

Tsohon gwamnan jihar Kebbi, Saidu Dakingari ya sanar da dalilan da suka sanya shi barin jam’iyyar PDP zuwa jam’iyya mai mulki ta APC.

Saidu Dakingari tare da tsohon mataimakinsa Ibrahim Aliyu da daruruwan magoya bayansu ne suka sauya sheka zuwa jam’iyya mai mulki inda suka samu kyakyawan tarba daga shugaban jam’iyyar na jihar Kebbi Alhaji Attahiru Maccido a filin buga kwallon Haliru Abdul a Birnin Kebbi.

A hirar da tsohon gwamnan ya yi da manema labarai, ya jadadda cewa ya yanke shawara sauya sheka ne sakamakon wani dogon tunani da ya yi bayan da ya bar mulki.

Dalilin da yasa na sauya sheka zuwa Jam’iyyar APC – Dakingari
Dalilin da yasa na sauya sheka zuwa Jam’iyyar APC – Dakingari

Ya bayyana cewa ba wai ya koma jam’iyyar APC don radin kansa ba, sai don kyawawan ayyukan shugaba Muhammadu Buhari a matakin gwamnatin tarayya da na Gwamnan Atiku Bagudu a jihar Kebbi.

KU KARANTA KUMA: An rantsar da George Weah a matsayin shugaban kasar Liberia (hoto)

Ya kara cewa “Ina kira ga dukkanin wadanda na yiwa ba dai dai ba da su yafe min inda ni kuma na yafewa dukkanin wadanda suka min ba dai dai ba.”

Tsohon gwamnan ya sha alwashin yin mai yiwuwa wajen ganin cewa jam’iyyar APC ta samu nasara a shekarar 2019

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng