Kuma dai! An sake gano cewa Diezani ta saci $1.3b daga asusun NNPC
- Hukumar EFCC ta bankado wasu makudan kudi da tsohuwar ministan mai ta sata
- Tsohuwar ministar dai ta boye a kasar Landan inda take buya
Da alamun badakalar da akayi a gwamnatin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, bai gama fitowa ba har yanzu yayinda aka gani wani sabon biliyoyin kudin da tsohuwar ministan mai, Mrs. Diezani Alison-Madueke, ta yi a kamfanin NNPC.
Hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC ta gano cewa Mrs. Diezani Alison-Madueke.ta cire $1.3billion daga asusun NNPC da sunan yakan garkuwa da mutane da kuma tabbatar da tsaro a yankin Neja Delta.
Ta cire wannan makudan kudi ba tare da izinin majalisar dokoki ba ko majalisar zantarwa.
Hukumar EFCC ta binciki wani tsoshon shugaban bangaren kudi na kamfanin NNPC, Mr. Bernard Otti, a kan fitan kudin. Otti ya baiwa hukumar takardun hujja da dama wanda ya kunshi $1.3billion da Mrs Alison-Madueke ta cira.
A wani bincike kuma, Jonathan ya umurci tsohuwar ministar ta amshi kudi daga asusun NNPC.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng