Alexis Sanchez zai kwashi makudan miliyoyi a Manchester United

Alexis Sanchez zai kwashi makudan miliyoyi a Manchester United

- ‘Dan wasan zai tattara ya koma bugawa Koci Jose Mourinho

- Alexis Sanchez ya ki sabunta kwangilar sa da Arsene Wenger

- 'Dan wasan zai tashi daga Arsenal zuwa Man Utd kwanan nan

Mun samu labarin yadda ‘Dan wasa Alexis Sanchez zai kwashi makudan miliyoyi a matsayin albashin sa kowane mako a Kungiyar Manchester United inda ake sa rai zai koma taka leda cikin 'yan kwanaki kadan masu zuwa.

Alexis Sanchez zai kwashi makudan miliyoyi a Manchester United
‘Dan wasa Sanchez zai koma bugawa Mourinho

Kungiyar Manchester ta Jose Mourinho za ta biya ‘Dan wasan na Kasar Chile sama da fam miliyan £350, 000 a kowane makon Duniya. Bayan nan kuma ‘Dan wasan mai shekaru 29 a Duniya na iya karbar wasu garabasa idan an dace a kulob din.

KU KARANTA: Gwamnatin Amurka ta tsaya cak a farkon shekara

Babban ‘Dan wasan gaban ya ki amincewa da sabon kwantiragi a Arsenal ne inda ya amince ya koma Manchester United. Tsohon Kocin sa Pep Guardiola yayi kokarin kawo ‘Dan wasan gaban zuwa Manchester City a watan nan.

Idan har Arsenal tayi sake, Sanchez zai tashi araha banza inda za tayi biyu-babu don haka ta saida shi cikin kaka kan kudin da ya kai fam Miliyan £35. Ana za ran kuma ‘Dan wasan tsakiya Henrikh Mkhitaryan ya koma Arsenal.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng