Rikicin Makiyaya: An fallasa asirin Gwamnan Jihar Benuwe

Rikicin Makiyaya: An fallasa asirin Gwamnan Jihar Benuwe

- Wata Kungiya ta zargi Gwamna Ortom da hannu cikin rikicin Benuwe

- Kungiyar tace da gangan ake kalawa Makiyaya laifin kisan Bayin Allah

- Kwanaki Sojoji sun kama wasu da Gwamna Ortom ta horar su na ta’asa

Mun samu labarin yadda Gwamnan Benuwe watau Mai Girma Samuel Ortom ke hura wutan rikicin Jihar sa. Ana zargin Gwamnan da kokarin ganin bayan wasu kabilu da ke Jihar ta amfani da kudin al’ummar Jihar a wata makarkashiya.

Rikicin Makiyaya: An fallasa asirin Gwamnan Jihar Benuwe
Gwamna Ortom ke hura wutan rikicin Jihar Benuwe

Daily Times ta kawo wani rahoto na cewa Gwamnan Benuwe Samuel Ortom ya shirya amfani da wasu ‘Yan iskan gari da Gwamnati ta ba makamai domin kauda sauran kananan kabilun da ke zaune a Jihar sa da sunan Makiyaya Fulani.

KU KARANTA: Matar Shugaban kasa Buhari ta na da basira - Murray Bruce

Shugaban wata Kungiya GGTI mai suna “Good Governance and Transparency Initiative” Jaiyeola Mohammed tace Gwamnan ne ke da laifi wajen hare-haren da ake kai wa mutanen Jihar sa kana sai ya koma baya yana kukan karya.

An dai zargin Gwamnan da yunkurin kashe sama da Naira Biliyan guda wajen yada furofaganda a kasashen waje irin su Ingila da Amurka da su Kanada domin shafawa Fulani bakin jini na kisan Jama’a alhali akwai hannun sa a rikicin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng