An ga jirgi mai saukan angulu ya kawo makamai jihar Taraba
An ga wani jirgi mai saukan angulu da ake zargin yana dauke da makamai jiya daddare ya sauka a wani kauye mai suna Jibo kusa da Ibi, karamar hukumar Wukari na jihar Taraba.
Babban mai magana da yawun gwamnan jihar Taraba, Mr. Bala Dan-Abu, ya bayyanawa manema labarai cewa an kawo makaman ne domin baiwa yan ta’adda su kai hare-hare wasu kauyukan jihar Taraba.
“Irin wannan kawo makamai ya faru a bara lokacin da aka kai hari garin Agatu a jihar Benue inda aka hallaka jama’a da dama."
“Lokacin da aka ba da rahoton, ba’a dau wani mataki ban a kama masu jirgin. Wannan abu yayi ma yan ta’addan amfani kuma suna kara amfani da shi yau. Da alamun suna shirin kai wani hari akan jama’an jihar Taraba.”
Dan majalisan dokokin jihar mai wakiltan Wukari, Hon. Josiah Aji,a wani hiran wayan tarho ya tabbatar da wannan labari ga jaridar Punch ranan Lahadi inda ya an sanar da si akan wannan abu.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng