Fadar Shugaban kasa ta bayyana dalilin da ya sa asibitin ta ya sukurkuce
- Gwamnatin Buhari za ta gyara asibitin Fadar Shugaban kasa
- An ware kusan Miliyan 700 Inji wani Babban Jami'in Fadar
- Sai da ta kai kwanakin baya babu magani a babban asibitin
Mun ji cewa ana sa ran a shekarar nan za a gyara asibitin Fadar Shugaban kasa bayan Uwargidar Shugaba Muhammadu Buhari watau Hajiya Aisha Buhari ta kai kuka kwanakin baya.
Wani babban Jami'in Gwamnati a Fadar Shugaban kasar na Aso Villa Malam Jalal Arabi ya bayyanawa wasu Sanatocin kasar wannan a karshen makon nan da ya je kare kasafin kudin Fadar Shugaban kasa na shekarar bana.
KU KARANTA: Ubangiji ya jarabci Shugaba Buhari a bara da ciwo a bara - APC
Jalal Arabi yace a bara ba a warewa asibitin ko sisi ba kuma an duba marasa lafiya sama da 44,000 a kyauta. Sanata Tijjani Kaura yace bai dace a rika aiki a kyauta ba yayin da ake neman kudin magunguna da gyaran asibitin.
Arabi yace wannan shekarar dai za a kashewa asibitin Naira Miliyan 698. Arabi yace ko ficika marasa lafiya ba su biya a asibitin. Sanatan na APC ya nemi ayi rangwame amma ba 100-bisa-100 ba domin gyara harkar lafiya.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhaus
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng