Aisha Buhari mace ce mai basira - Ben Bruce
- Sanata Ben Bruce ya yabawa Aisha Buhari akan saka bidiyon da ya nuna ana sukar Buhari a shafin ta na tuwita
- Ben Burce ya shawaric Aisha Buhari kada ta bari masu sukar ta su bata tsaoro
Senata mai wakiltar mazabar Kudancin jihar Bayelsa, Ben Murray-Bruce, yace, uwar gidan shugaban kasa, Aisha Buhari mace ce mai basira da za ta iya shugabanci da kyau.
Senata yayi wannan jawabin ne akan wasu bidiyo da Aisha ta saka a shafin ta na Tuwita a ranar Alhamis na makon da ya gabata.
Bidiyon ya nuna Sanata Misau da Sanata Ben Bruce suna sukar shugaba Buhari akan rikicin makiyaya da manoma da ya addabi kasar.
KU KARANTA : Barayin sun kona wani yaro mai shekaru 12 a jihar Kogi
Sanata Murray Bruce ya shawarci Aisha Buhari da kada ta bari masu sukar ta su bata tsoro saboda ita ba matar uwar 'daka bane.
Murray Bruce ya bayyana haka ne a shafin sa na tuwita a ranar Juma’a 19 ga watan Janairu, 2018.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng