Gwamna Tambuwal ya kaddamar da fara sayar da takin da aka sarrafa a jihar Sokoto
- Gwamna Tambuwal ya kaddamar da fara sayar da takin noma da aka sarrafa a jihar Sokoto
- Gwamnatin jihar da hadin gwuiwar wani kamfani su ka sarrafa takin
- An kirkiri takin ne daga sinadaran takin gargajiya na Bahaushe
Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya kaddamar da fara sayar da takin noma da aka sarrafa a jihar, gwamnatin jihar da hadin gwuiwar wani kamfani, Sokoto-IML, su ka samar da takin.
Da yake jawabi yayin kaddamar da fara sayar da takin, Tambuwal, ya ce samun nasarar kamfanin alama ce ta kokarin gwamnatinsa na gina tattalin arzikin jihar Sokoto.
Tambuwal ya ce, jihar Sokoto na daga cikin jihohin Najeriya da Allah ya yi wa baiwa da ma'adanai masu matukar muhimmanci, kuma hakan ne ya saka gwamnatinsa hada gwuiwa da kamfanin domin samar da takin daga sinadaran takin gargajiya na Bahaushe.
Kazalika ya yi albishir din saya wa kafatanin kananan hukumomin jihar tirela hudu na samfurin sabon takin da aka yi kiyasin kudinsa ya wuce miliyan N100m.
DUBA WANNAN: Ku kalli yadda gwamnatin jihar Sokoto ta yi ruwan kayan aiki ga makarantun jihar
Da yake tofa albarkacin bakinsa, babban manajan darektan kamfanin, Alhaji Bilya Sanda, ya ce idan kamfanin ya fara aiki gadan-gadan, zai ke samar da kimanin buhu 20,000 na taki kowacce rana.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng