Jihohi da za a fafata manyan yaƙe-yaƙe a siyasar 2019
A yayin da amo tare da sauti na gangunan siyasa suka fara tashi a faɗin ƙasar nan, shirye-shiryen fitar da 'yan takara na zaɓen 2019 ya fara kankama, inda tuni manyan 'yan siyasa da masu riƙe da kujerun mulki suka ɗauki sulke tare da ɗaura ɗamarar yaƙi na fafatawa a zaɓen ƙasa mai gabatowa.
Da sanadin jaridar Daily Trust, Legit.ng ta fahimci cewa, tuni shirye-shiryen zaɓe sun yi nisa a wasu jihohin, a sakamakon da hukumar zaɓe ta ƙasa ta shar'antawa jam'iyyun siyasa a kan su kammala tsayar da 'yan takarar kujerar shugaban ƙasa, gwamnoni tare da 'yan majalisun jiha da na tarayya a zaɓen mataki na farko a watan Oktoba na shekarar 2018.
A jadawalin da hukumar INEC ta fitar dangane da babban zaɓe na ƙasa, za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da 'yan majalisun tarayya a ranar 16 ga watan Fabrairun 2019, inda zaɓen gwamnoni da 'yan majalisu na jiha zai biyo baya a ranar asabar, 2 ga watan Maris na shekarar ta 2019.
KARANTA KUMA: Dole sai gwamnati ta yi la'akari da fushin kowace ƙabila - Inji Obasanjo
Legit.ng da sanadin hasashe na mahanga ta shafin jaridar Daily Trust, ta kawo muku jerin yake-yake da za a fafata dangane da gabatowar zaɓen ƙasa na 2019.
1. Jihar Bauchi
2. Jihar Nasarawa
3. Jihar Imo
4. Jihar Akwa Ibom
5. Jihar Yobe
6. Jihar Legas
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng